Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC, ta roƙi Gwamnatin Jihar Kano da ta gyara tare da inganta sansanin hukumar na dindindin da ke Kusalla Dam, a Ƙaramar Hukumar Karaye.
Ko-odinetar NYSC ta Jihar Kano, Halima Abubakar Abdulkareem, ce ta yi wannan roƙo bayan rantsar da matasan Batch B Stream Two na shekarar 2026 a sansanin.
Hajiya Halima ta gabatar da buƙatun ne yayin da ta raka Kwamishinan Ma’aikatar Bibiyar Ayyukan Gwamnatin Kano, Comrade Nura Ma’aji Sumaila, wajen duba muhimman wuraren sansanin.
Ta ce sansanin na buƙatar gyaran ɗakunan kwanan maza da mata, gidajen jami’ai, asibiti da babban ɗakin taro, da kuma ƙarin katangar da ke kewaye da sansanin.
Ta kuma buƙaci samar da inuwa a wuraren girki domin inganta jin daɗin matasan da jami’an da ke sansanin.
Da yake mayar da jawabi, Kwamishinan Ma’aikatar Bibiyar Ayyukan Gwamnatin Kano, Comrade Nura Ma’aji Sumaila, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa zai isar da buƙatun ga gwamnan domin a duba yiwuwar ɗaukar matakin gaggawa.
