Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na Uku, ya ƙaddamar da manhajar EasyZakat, wadda aka ƙirƙira domin inganta gaskiya, riƙon amana da inganci wajen karɓa da rabon Zakka a faɗin ƙasar.
An ƙaddamar da manhajar ne a Abuja ta hannun Sarkin Keffi, Dakta Shehu Usman Chindo Yamusa na Uku, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi.
A cikin jawabin da ya gabatar a madadin Sarkin Musulmi, Sarkin Keffi ya ce amfani da fasahar zamani wajen gudanar da harkokin Zakka zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da sauƙaƙa bayar da Zakka da tabbatar da cewa ta isa ga waɗanda suka cancanta.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa amfani da fasahar zamani wajen tafiyar da harkokin Zakka zai taimaka wajen rage talauci, ƙarfafa tsarin jin daɗin al’umma da kuma bunƙasa rayuwar Musulmi a Najeriya.
Sun ce manhajar EasyZakat na da damar sauƙaƙa tsarin bayarwa da rarraba Zakka, tare da samar da ingantaccen tsarin bin diddigin yadda ake tafiyar da kuɗaɗen Zakka.
