Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso ya nada Daurawa limamin sabon masallacinsa

Kwankwaso ya nada Daurawa limamin sabon masallacinsa

Date:

Tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya nada Malam Aminu Ibrahim Daurawa Limamin Masallacin juma’ar da ya gina a gidansa.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da gidauniyar Kwankwasiyya ta fitar ranar Lahadi.

 

Sanarwar ta ce an nada Daurawa ne tare da wasu Malamai 7 a matsayin limamai da mataimaka.

 

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar da ta gabata ne Kwankwaso ya kaddamar sa sabon Masallacin ya Kuma ce ya baiwa al’umma kyauta.

 

Sanarwar takara da cewa wadanda aka nada din sun hadar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin Babban Limami kuma Shugaba.

 

Sai Sheikh Sadiq Isa Abdullahi da Sheikh Gwani Baffa Ite da kuma Sheikh Bazallah Nasir Kabara a matsayin limamai.

 

Sauran su ne Dr. Sani Ashir a matsayin Mamban kwamitin masallacin, da Dr Muhammad Khamis Hussain a matsayin Sakatare.

 

Sai Sheikh Nura Abdullahi Salihu a matsayin Dan Majalisa da Kuma Malam Ashir Nata’ala limamin kamsusalawat.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...