33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiZargin kai hari:DSS ta bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu

Zargin kai hari:DSS ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci al’umma su kwantar da hankulansu kan sanarwar da ofishin jakadancin Amurka ya fitar na shirin kai hari a Abuja.

 

Wannan na kushe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Peter Afunanya ya fitar ranar Lahadi.

 

Afunanya ya ce dama hukumar ta DSS ta dade tana bada irin gargadin ga jama’a.

 

A don hakan ne ya bukaci al’umma da su dauki matakin kula da duk wani abu da basu yarda dashi ba.

Ya kuma bukaci jama’a da su taimakawa jami’an tsaro wajen kai rahoton duk wani abu da suke ganin zai basu barazana ko kuma Wanda basu yadda da shi ba.

 

Haka Kuma hukumar ta bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa inda ta ce tana aiki kafada da kafada da sauran jamia’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Abuja da ma kasa Baki Daya.

Latest stories