Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJami'o'i hudu ne suka baiwa amaryata gurbin karatu-Sheikh Daurawa

Jami’o’i hudu ne suka baiwa amaryata gurbin karatu-Sheikh Daurawa

Date:

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan na Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce jami’o’i huɗu ne suka ba amaryarsa gurbin karatu kyauta.

 

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani gajeren bidiyo da Premier Radio ta gano shi a shafin TikTok.

 

Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Malam Daurawa ya auri Malama Haulatu Aminu Ishaq a Gusau, baban birnin jihar Zamfara.

 

Amaryar dai mahaddaciya ce kuma gwanar Ƙur’ani Mai Girma.

 

“Yanzu akwai wata jami’a daga ƙasar Indiya suka zo suka buɗe reshensu a Kano, Skyline University. Da suka samu labari an ce na auro hafizar Alƙur’ani suka ce sun ba ta gurbin karatu ta yi karatu kyauta.

 

“Miliyan N12 ake biyawa ɗalibi kafin ya yi digiri, jami’a mai zaman kanta.

 

“Yanzu suka turo min ta waya cewa wannan matar taka Malam, mun ba ta gurbin karatu za ta yi karatu a wannan jami’ar kyauta.

 

“Jami’ar Bayero sun kira ni su ma, ta dawo ta yi karatu a BUK. Haka Jami’ar Khadijah suka ce sun ba ta ita ma ta je ta yi digiri a can”, in ji Malam Daurawa.

 

“Yanzu na samu gurbin karatu kusan huɗu. Na ba ta ɗaya na ba marayu guda ukun.

 

“Me yasa wannan? Darajar ilimi”, in ji shi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories