Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGudun satar amsa ya sa naki bayyana manufata-Kwankwaso

Gudun satar amsa ya sa naki bayyana manufata-Kwankwaso

Date:

Dantakarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya jinkirta bayyana manufofin siyasarsa ne don gudun satar amsa.

 

Kwankwaso ya bayyana hakan ne ya yin da yake zantawa da sashin Hausa na BBC.

 

Ya ce suna nan suna shirin fito da tsari mai kyau da ya banbanta da na sauran yan takara a kasar nan.

 

“Za mu fito ne da tsari wanda ya banbanta da na sauran an takara.”

 

“Za mu fito da tsarin abin da za mu yi, da kuma yadda za mu aiwatar da shi.” Inji shi.

 

Kwankwaso ya ce ya shiga dukkanin manyan jam’iyyun kasar nan biyu (APC da PDP) amma ya dawo daga rakiyarsu saboda sun gaza samar da manufofin da za su ciyar da ƙasar nan gaba.

 

Ya kuma yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya ƙi amsa gayyatar ƙungiyoyin Arewa domin bayyana ƙudurorinsa ga yankin.

 

A cewar sa “…shi ya sa aka kafa tarko a Kaduna, suna so idan na je na yi bayani, daga baya su ce ga wani ɗan takara shi ya fi cancanta.”

 

Yan takarar shugaban kasa hudu ne suka halarci tattaunawar, wadda gamayyar kungiyoyi masu kare muradun arewacin kasar nan suka shirya a gidan tsohon firaiministan yankin, Ahmadu Bello.

 

Kungiyoyin da suka shirya taron sun ce manufarsu ita ce su ji bayanai daga yan takara kan tanadin da suka yi wa yankin, sannan su fadawa yan takaran nasu bukatun.

 

Kuma sun musanta duk wasu zarge-zargen cewa sun shirya taron ne domin nuna goyon baya ga wani dan takara.

 

Latest stories

Related stories