Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAmbaliyar ruwa: Tinibu ya tallafawa 'yan Kano da mil'yan 100

Ambaliyar ruwa: Tinibu ya tallafawa ‘yan Kano da mil’yan 100

Date:

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Kano.

 

Tinubu, ya bayar da tallafin ne yayin wata liyafar dare da kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano ta shirya domin karrama shi.

 

Ya ce ya bayar da tallafin ne a yunkurinsa na taimakawa wajen rage radadin ambaliyar ruwa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

 

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Kano ta bayyana cewa, an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 19 cikin 44 na Kano, inda mutane 23 suka mutu, 106 suka jikkata, sannan gidaje 12,919 sun rushe yayin da gonaki 14, 496 suka lalace a kananan hukumomi biyar daga ciki.

 

Da yake jawabi a wurin liyafar, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa bambance-bambancen Najeriya ya zama tushen samar wa kasa arziki idan ya zama zababben shugaban kasa a 2023.

 

Tinubu ya yi alkawarin sake dora masana’antun kasar nab a kan turbar gogayya da takwarorinsu na duniya ba kawai ga Arewa ko Kano ba har ma da kasa baki daya.

 

Ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar, inda ya bayyana gwamnan a matsayin “aboki kuma amintaccen abokin tarayya.”

 

Ya kuma yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...