Rundunar Sojin Najeriya ta ce akalla kwamandojin ƙungiyar ISWAP 76 ne suka miƙa wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas.
Rahotanni sun ce waɗanda suka miƙa wuya sun haɗa da manyan kwamandoji da mayaka, lamarin da rundunar ke kallon a matsayin wani gagarumin ci gaba a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
An ce mutanen sun mika makamansu tare da amincewa su shiga bincike da tantancewa na hukumomin tsaro.
A cewar rundunar, ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta ƙasa kan maɓoyar ‘yan ta’addan, tare da katse hanyoyin samun kayan aiki da abinci, na daga cikin abubuwan da suka tilasta wa mayakan barin dazuka da miƙa wuya.
Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP lamba har sai an dawo da cikakken zaman lafiya a yankunan da matsalar ta fi kamari. Ta kuma buƙaci sauran mayakan da ke cikin dazuka su yi koyi da waɗanda suka miƙa wuya, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas.
