Akalla mutum 12 ne suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Warawa. Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne bayan wata takaddama tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya rikide zuwa faɗa tare da jikkata mutane da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin manoman ƙauyen Larabar Gadan Sarki da makiyaya daga ƙauyukan Majawa da Karade. Wadanda suka jikkata, sun samu raunuka daban-daban, yayin da jami’an tsaro suka garzaya wurin domin daƙile rikicin da hana yaɗuwarsa zuwa sauran al’ummomin da ke makwabtaka dasu.
Hukumomin tsaro sun ce sun fara bincike kan musabbabin rikicin, tare da ɗaukar matakan tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Sun kuma fara tattaunawa da shugabannin al’ummomin da abin ya shafa domin hana sake aukuwar irin wannan rikici.
Masu ruwa da tsaki sun sake jaddada muhimmancin warware rikice-rikicen manoma da makiyaya ta hanyar tattaunawa, tare da kira ga al’ummomin yankin da su guji ɗaukar doka a hannunsu, su riƙa kai rahoton duk wata takaddama ga hukumomin da abin ya shafa.
