Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ta EFCC, ta shigar da ƙarar tsoffin daraktocin matatun mai na Fatakwal da Warri, bisa zargin halasta kuɗaɗen haram, bayan karkatar da kuɗaɗen da aka ware don gyara matatun man.
RFI ta rawaito cewa, EFCC ta gurfanar da tsohon daraktan da ke kula da matatar man Fatakwal, Ahmed Adamu Dikko, da takwaransa da ke kula da matatar Warri, Jimoh Olasunkanmi Yisawu gaban kotu.
Takardun kotun da jaridun suka gani, ya nuna cewa EFCC na tuhumar Dikko da laifuka 12, sai Yisawu mai laifuka 8 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Hukumar na zargin tsoffin daraktocin biyu da karbar na goro daga hannun ƴan kwangilar da kamfanin mai na kasa NNPC ya ɗora wa alhakin kula da gyaran matatun, sannan sun mallakin asusun banki da ake amfani dasu wajen halasta kuɗaɗen haram, wanda ya saɓa da dokokin ƙasa.
Waɗannan zarge-zarge na zama wani sabon ci gaba, a binciken da EFCC ta ce tana yi don gano waɗanda suka handame biliyoyin kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta fitar a wancen lokacin don gyara matatun, da har kawo yanzu basa aiki.
Ya zuwa yanzu, hukumar ta samu nasarar ƙwato wasu biliyoyin naira, da kadarori da dama daga hannun tsoffin jami’an NNPC, wanda ta bayyana a matsayin gagarumar nasara a yaƙin da take da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati.
