Gwamnatin Kano ta yi hadin gwiwa da Majalisar dinkin duniya da Tarayyar turai domin sabunta makamashi da ƙarfafa tattalin arziki da samar da ingantaccen tsarin sarrafa Shara da sauran makamashi.
Kwamishinan Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Kano, Dr Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron bita domin ƙarfafa ƙwarewa kan tsarin tattara bayanai na ƙasa kan sabbin dabarun sabunta makamashi marasa alaƙa da wutar lantarki ta gwamnati.
Da yake jawabi a wajen taron na kwanaki biyu wanda Kano ke karɓar bakuncin, Dr Hashim ya ce sauyin da ake samu zuwa sabunta makamashi dole ne ya kasance tare da ingantaccen tsarin zubar da kaan da suka lalace kamar hasken rana batira da sauran kayan makamashi.
Ya kuma bayyana cewa Kano na ƙara ƙarfafa tsarin kula da muhalli ta hanyar manufofin sauyin yanayi, gyaran dokoki, amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan muhalli, da kuma ayyukan gyaran muhalli, ciki har da shirin dasa bishiyoyi miliyan 10 a wannan shekara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishinan na cewa gwamnati na farfaɗo da wuraren shakatawa, inganta tsarin tara shara ta hanyar raba shara rzuwa launuka daban-daban, gyara cibiyar sarrafa shara ta Dorayi, da kuma kafa cibiyar masana’antar sabunta makamai a Gabasawa wadda ake sa ran za ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin irin ta a Najeriya.
