Saurari premier Radio
32.7 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar shugaba Bola...

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Date:

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Kotun, wadda ta gabatar da hukuncin a daren jiya Laraba a Abuja, ta yi watsi da korafe-korafen da yan takarar shugabancin kasa a zaben, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar Labour suka shigar na neman soke zaben shugaba Tinubu.
Babban alkalin kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani, ya ce matakin hukumar zabe na ayyana Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben ya dace.
Wakilinmu, Shehu Usman Salihu, na dauke da karin bayani kan yadda aka karkare zaman shari’ar bayan shafe wunin jiya ana yanke hukuncin.

Manyan jam’iyyun hamayyar kasar nan biyu PDP da LP sun ce za su daukaka kara bayan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na jiya Laraba, da ya tabbatar da Bola Tinubu na APC a matsayin halastaccen shugaban kasa.
Kotun ta shafe yinin jiya tana hukunci kan karar da Peter Obi na LP da Atiku Abubakar na PDP suka shugar mata inda suke kalubantar nasarar shugaba Tinubu a zaben da ya gabata.
Ibrahim Haruna Ibrahim babban jigo ne a jam’iyyar LP a nan Kano, a tattaunawar sa da wakilin mu Faisal Abdullahi Bila, yace basu ji dadin hukuncin kotun ba kuma kamar yadda sanarwa ta bayyana, za su daukaka kara.

Dama dai masana shari’a irin su Abba Hikima fagge na ganin ba lallai a samu sauyi a hukuncin kotun ba dangane da nasarar shugaba Tinubu.

A nasa bangaren shima dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin tafiya kotun koli domin sake kalubalantar nasarar Tinubu a zabe.
Atiku dai ya nuna rashin gamsuwarsa da hukuncin kotun kararrakin zabe, da ya tabbatar da ya tabbatar da nasarar zaben Tinubu.
Ta bakin jagoran lauyoyinsa a shari’ar, Chief Chris Uche SAN, Atiku ya ce sun samu hukunci amma ba adalci ba, kuma kundin tsarin mulki ya basu damar daukaka kara.
Itama jam’iyyar da Atikun ya yiwa takara PDP ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke na tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa.
A wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba bayan yanke hukuncin, mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta Debo Ologunagba, PDP ta ce ta yi nazari kan hukuncin kuma ba ta yarda da shi ba gaba daya.

Sai dai batun da yan jamiyyar Hammayyar suke na daukaka kara bai hana shugaba Tinubu murnar hukuncin kotun ba.
A wani video da aka yada an gano Tinubu da mukarrabansa na sowa tare da raira masa wakokin taya murna kan hukuncin.

Tinubu dai wanda ke halartar taron kasashen G20 a kasar India yanzu, an nuno shi ya na kallon yadda zaman kotun ke gudana har a kai ga yanke hukuncin.

Shima mataimakin shugaban kasa, Kashim Shattima ya bayyana farin cikin da hukuncin da ya basu nasara.
Bayan shafe wuni guda yana halartar zaman kotun, Shettima ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa ba’a taba yin sahihin zabe a kasar nan kamar wanda ya gabata ba.

A nasa bangaren shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ko kotun gaba aka je ya na da yakini su za su yi nasara.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin da kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar ta kafa tarihi ta hanyar yin watsi da duk wata barazana da zargi marar tushe wajen yanke hukunci cikin gaskiya da adalci, don martaba zaɓin ‘yan Najeriya.

Buhari ya ce “duk wanda ya yi nasara a yau dimokraɗiyya da al’umma ne suka yi nasara, idan Kotun Ƙoli ta yanke hukunci, to an gama da batun zaɓe lokaci ne da ya kamata ƙurar zaɓe ta kwanta”.

Toshon shugaban ƙasar ya kuma aike da saƙon taya murna ga shugaban ƙasar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da kuma jam’iyyar APC kan wanna nasara da suka samu a kotu.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...