Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci kungiyar Kwadago ta kasa...

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar nan, kan ta sassauta ga bangarorin da suka kasance mafiya bukatuwa ga al’umma yayin yajin aikin gargadi da suka fara na kwana biyu.

Date:

Shugaban ma’aikatan jihar Kano, Alhaji Usman Muhammad ne ya mika rokon a madadin gwamnan, cikin wata sanarwa da Daraktar yada labarai a ofishin shugaban ma’aikatan Hajiya Bintu Yakasai ta fitar, tare da rabawa manema labarai.
Alhaji Usman ya ce gwamnati mai ci tamkar ƙawace ga kungiyar Kwadago, a don haka a shirye take domin ganin ta marawa kungiyar baya a dukkan ayyukan da ta sanya gaba, wadanda suke da nufin saukakawa al’umma domin kowa ya samu sauki.
Da yake jawabi yayin taron da kungiyar Kwadagon tayi da shugaban ma’aikatan dangane da halin da ake ciki, shugaban kungiyar reshen Kano, Kabiru Inuwa ya godewa Gwamna Abba Kabeer Yusuf dangane da irin yadda ya baiwa ma’aikata fifiko, da kuma yadda ya taimaki rayuwar yan fansho na jiha baki daya.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories