Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMasu kamfanonin da kan sarrafa kayayyakin bukata na yau da kullum anan...

Masu kamfanonin da kan sarrafa kayayyakin bukata na yau da kullum anan Kano, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha, kan su duba bangare masu karbar haraji a wajen su, domin samar da nagartaccen tsari, wanda zai tamaka wajen ganin sun samu saukin bayar da harajin.

Date:

Masu kamfanonin da kan sarrafa kayayyakin bukata na yau da kullum anan Kano, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha, kan su duba bangare masu karbar haraji a wajen su, domin samar da nagartaccen tsari, wanda zai tamaka wajen ganin sun samu saukin bayar da harajin.
Shugaban kamfanin sarrafa shinkafa na Alwabel Alhaji Imrana Muhammad Amin, na daga cikin masu irin wannan kira, yayin tattaunawarsa da Premier Radio, dangane da yadda ake ci gaba da samun karuwar farashin shinkafa, duk kuwa da cewa manoma da masu sarrafa shinkafar duk a Kano suke.
Alhaji Imrana Muhammad Amin, ya ce yawan rubdugun da akan samu wajen karbar harajin yana taimakawa wajen ganin abubuwa sun kara tsada ga kamfani, wanda shi kuma kamfani dole ya duba farashin da zai fi zama mafita gare shi, domin dorewarsa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu, kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas, ya ce gwamnatin Kano tuni tayi nisa wajen samar da tsarin fara tantance adadin yan kasuwa da kamfanonin da ake da su a jihar, wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen magance wannan matsala.

Alhaji Imrana Muhammad Amin, ya kuma bukaci gwamnati ta kara yawan samar da bashi ga yan kasuwa mai saukin kudin ruwa, wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen kara habbaka kasuwancin da dama cikin yan kasuwa da ma kamfanoni baki daya.

Latest stories

Related stories