Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace karuwar makaratun kimiya da...

Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace karuwar makaratun kimiya da fasaha da ake yi a jihar nan hakan ka iya kawo cigaba mai dorewa a fannin ilimi

Date:

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace karuwar makaratun kimiya da fasaha da ake yi jihar nan hakan ka iya kawo cigaba mai dorewa a fannin ilimi duba da yadda ilimi shine madubin rayuwa tare da nuna farin cikin sa da yadda gwamnatin tarayya data kara bude sababbin makarantun kimiya da fasaha wato Polytechnic a kasar nan domin bunkasa fannini kimiya .
Sarki na Kano ya bayyana haka ne lokacin da sabon shugaban makarantar kimiya da fasaha ta kabo Farfesa Muhammad Sunusi Magaji ya ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma kara da cewa yawaitar makarantar kimiya da fasaha zai bunkasa fannin tatattalin arzikin kasar nan tare da koyawa matasa yadda zasu dogara da kansu da kuma kere-keren a fannin na kimiya a fasaha.

A nasa jawabin sabon shugaban makarantar Farfesa Muhammad Sunusi Magaji wannan makarantar sabuwa kuma an kirkiro ta ne domin gannin yadda matasan marasa aikin yi suken kara yawa wanda hakan zai taimaka musun wajen dogaro da kan su ta hanyar kere-kere batare da jiran aikin Gwamnati ba.

mai martaba sarki ya yabawa gwamnatin tarayya da kara bude sababbin makarantun kimiya da fasaha a fadin kasar kasar nan tare da aduar samun zaman lafiya a kasa baki daya.

Latest stories

Related stories