Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace fiye da kadarori 40 da ake alaƙanta wa da tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da buƙatar Hukumar EFCC bayan ta ce waɗanda ake ƙara sun kasa kawo hujjojin da za su kawar da zargin cewa an mallaki kadarorin ne ta haramtacciyar hanya.
Kafin yanke hukunci, kotun ta yi watsi da duk wasu ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da Malami, iyalansa da wasu kamfanoni da ake alaƙanta da kadarorin suka gabatar, tana mai cewa ba su da ingantaccen tushe.
Mai shari’ar ta bayyana cewa batun da ke gaban kotun ba wai wanene ya mallaki kadarorin ba ne, sai dai ko kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin sun fito ne ta halastacciyar hanya.
Ta ce waɗanda ake ƙara ba su iya kawar da zargin EFCC cewa kadarorin sun samo asali ne daga ayyukan da suka saɓa wa doka.
A watan Janairun 2026 ne EFCC ta shigar da ƙarar neman a ƙwace kadarori 57 da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 212.8, tana zargin cewa kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen mallakarsu sun fito ne daga haramtattun ayyuka.
Kotun ta bayyana cewa kadarorin suna jihohin Abuja, Kano, Kebbi da Kaduna.
Bayan an wallafa sanarwar ƙwacen kadarorin, Malami, matarsa Nana Hadiza Malami, ɗansa Abdulaziz Abubakar Malami da wasu kamfanoni sun ƙalubalanci matakin, suna cewa kadarorin an same su ne ta hanyar halal kuma EFCC ba ta gabatar da hujjojin da ke nuna cewa sun samo asali daga wata laifi ba.
Sai dai EFCC ta dage cewa bincikenta ya nuna an mallaki kadarorin ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya, kuma an ɓoye mallakarsu ta hanyar amfani da sunayen wasu mutane da kamfanoni.
Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, kotun ta yanke hukuncin ƙarshe a ranar Laraba, inda ta amince da ƙwace mafi yawan kadarorin ga Gwamnatin Tarayya.
