Jihar Kano ta samu tikitin halartar wasu daga cikin gasar wasanni ta ƙasa karo na 23 na shekarar 2026, bayan da ‘yan wasan jihar suka nuna bajinta a gasar tantance waɗanda za su wakilci shiyyar Arewa maso Yamma, da ke gudana a Kaduna.
A wasan Beach Volleyball, Kano ta samu tikitin zuwa gasar ƙasa bayan ta yi nasara a dukkan wasanni ukun da ta buga, inda ta doke Kaduna da ci 2-1, Sokoto da ci 2-0, sannan Zamfara da ci 2-0.
Haka kuma, a wasan Volleyball na yau da kullum, Kano ta samu gurbin zuwa gasar ƙasa bayan ta doke Zamfara da ci 2-0, sannan ta yi nasara a kan Kaduna da ci 2-1.
A bangaren kwallon kwando na maza kuwa, tawagar Kano ta samu tikitin zuwa gasar ƙasa, bayan ta yi nasara a kan Kaduna da ci 83 da 70, yayin da tawagar mata ta Kano ta sha kashi a hannun Kaduna da ci 46-39, inda za ta kara da Zamfara a wasan karshe, kuma nasara a wasan za ta tabbatar mata da tikitin zuwa gasar ƙasa.
A gefe guda, tawagar Kano ta kwallon kafa ta maza za ta ci gaba da neman gurbin shiga gasar ƙasa, yayin da za ta kara da Sokoto.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Kano Alhaji Muhammad Tukur Babangida, ya ce nasarorin da tawagar jihar ta samu sun samu ne sakamakon ci gaba da kulawa da tallafin Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ya ce hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin Kano ta samu ƙarin tikiti a gasar tantancewar shiyyar, wadda ita ce hanyar samun gurbin halartar Gasar Wasannin Ƙasa ta 23, da Jihar Enugu za ta karɓi baƙunci.
