Gwamnatin Kano ta ce za ta ci gaba da zuba jari mai yawa a fannin ilimi, tare da jaddada muhimmiyar rawar da malamai ke takawa wajen gina al’umma.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a cikin jawabin da ya gabatar a wajen bikin ranar malamai ta duniya da ƙungiyar malaman Najeriya, reshen Kano, ta shirya.
Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya wakilta, ya ce gwamnatin sa ta baiwa harkar ilimi muhimmanci, tare da ƙoƙarin inganta jin daɗin malamai da samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Ilimi na Kano, Dr Ali Haruna Makoda, ya ce ci gaban kowace al’umma na da alaƙa da ingancin ilimi, yayin da ya yi kira ga malamai da su ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Shi ma Shugaban Ƙungiyar Malaman Najeriya, reshen Jihar Kano, Kwamred Baffa Ibrahim Garko, ya yaba da tallafin gwamnatin jihar ga malamai, yana mai buƙatar ci gaba da ɗaukar matakan inganta walwala da ƙwarewar malamai.
