Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar ta gaza samar da tsaro mai inganci a filin wasa, abin da ya bai wa wasu damar kutsawa inda aka haramta shiga.
Haka zalika an hukunta Kano Pillars bisa hana magoya baya shiga kallon wasan ta na tsawon wasa uku.
Inda wasa ɗaya daga cikinsu zai kasance a wannan kakar, yayin da sauran biyun za su kasance a farkon kakar wasa mai zuwa.
Bugu da ƙari, wasu magoya bayan ƙungiyar sun shiga cikin filin wasa ba tare da izini ba, lamarin da ya saba wa ƙa’idojin gasar.
Lamarin dai ya faru a ranar Lahadi a wasan da Kano Pillars ta doke Rivers United 2-1 a gasar Firimiyar Najeriya NPFL.
Kunshin laifukan sune rashin samar da isasshen tsaro da ya sa aka taci Pillars miliyan 4
Munanan laifuka ga yan wasa miliyan 3, hai farda tsaiko da katsewar wasa miliyan 2
Halayya mara kyau da wasu suka aikata ya sanya aka ci tara ta miliyan 3
Gaza kulawa da sarrada magoya baya har suka ci zarafi, ya sa aka tarar miliyan 3
