Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun da kuma Umar Dangiwa, Ministan Gidaje da Raya Birane.
An sanar da sauyin ne cikin wata takarda daga Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, wanda ya tabbatar da gyare-gyare a muhimman ma’aikatun tattalin arziki.
A cewar takardar, an umarci Edun da ya mika ragamar aiki ga Taiwo Oyedele, wanda zai karbi mukamin Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki.
Ana sa ran Oyedele, wanda a baya ya kasance Karamin Ministan Kudi, zai fara aiki nan take.
Haka zalika, an bayyana Dr Muttaqha Rabe Darma a matsayin wanda aka nada kuma zai zama Ministan Gidaje da Raya Birane.
Takardar ta kuma umarci Dangiwa da ya mika aiki ga Karamin Minista a ma’aikatar kafin karshen ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.
Akume ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin karfafa hadin kai da inganta yadda ake gudanar da gyare-gyaren tattalin arziki karkashin shirin “Renewed Hope Agenda.”
