Shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu, Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar, ya yi kira ga al’ummar arewa da su mutunta tsarin karɓa-karɓar shugabancin ƙasa, tare da barin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru 8 da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi dama.
Yari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gidan Gwamnatin Kano, bayan ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Tsohon Gwamnan na Zamfara ya ce ya kamata ‘yan aewa su fahimci tsarin siyasar da ya kai shugabancin ƙasa zuwa Kudu a shekarar 2023, kasancewar marigayi sohon Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ɗan Arewa ne, ya mulki Najeriya daga 2015 zuwa 2023, kafin mulki ya koma Kudu ta hannun Tinubu.
Yari ya buƙaci ’yan arewa da kada su yi ƙoƙarin sauya wannan fahimtar siyasa bisa hujjar yawan al’ummar yankin, yana mai cewa mutunta tsarin zai taimaka wajen zaman lafiyar Najeriya.
Game da matsalolin tsaro da tattalin arziki, Yari ya ce bai kamata a jingina dukkan ƙalubalen ƙasar ga gwamnatin tarayya kaɗai ba, la’akari da cewa rashin tsaro matsala ce da ƙasashe daban-daban ke fuskanta ciki har da Amurka.
Dangane da tattalin arziki, Yari ya ce ya kamata ’yan Najeriya su duba sauye-sauyen da aka samu ta hanyar kwatanta yanayin tattalin arzikin ƙasar lokacin da Tinubu ya hau mulki a 2023 da halin da ake ciki yanzu.
