Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKamfanin man fetur na kasa zai samar da danyen man fetur...

Kamfanin man fetur na kasa zai samar da danyen man fetur ga matatar Dangote.

Date:

Kamfanin mai na kasa ya ce shirye shirye tuni sun kammala domin baiwa matatar mai ta dangote gangar danyen mai miliyan 6, a wani mataki na karfafa bangaren ta ce man a cikin gida, maimakon kai shi zuwa kasar waje da nufi a ta ce.

Wani rahoto na musamman da jaridar Punch ta gudanar ya bayyana cewa, karancin danyen mai da matatar ke fuskanta, ya taka rawa wajen koma bayan matatar a ayyukanta, lamarin da ake ganin hakan tamkar abin kunya ne.

To sai dai a wani mataki mai kama da martani kan wannan batu, kamfanin man y ace zuwa nan da watan disamba wato karshen shekarar nan, zai fara baiwa matatar danyen mai ganga milyan 6.

Wani kusa a kamfanin da ya bukaci a asakaya sunasa, ya shaidawa manema labarai cewa, wannan bayar da danyen man ga matatar wani bangare ne na yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma tsakanin matatar da kuma kamfanin kwanakin baya a Abuja.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories