Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar Kwastam ta Jihar Kano tace a ranar Alhamis ta tara sama...

Hukumar Kwastam ta Jihar Kano tace a ranar Alhamis ta tara sama da Naira biliyan 38 a matsayin kudaden shiga daga watan Janairu zuwa Oktoba.

Date:

Hukumar Kwastam ta Jihar Kano tace a ranar Alhamis ta tara sama da Naira biliyan 38 a matsayin kudaden shiga daga watan Janairu zuwa Oktoba.

Dauda Ibrahim Chana, Kwanturolan hukumar dake kula da shiyyar Kano da Jigawa ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN.

Chana ya ce rundunar ta kama haramtattun kayayyaki na kimanin Naira miliyan 300 a cikin watanni 20 da suka gabata.

Kayyayakin da suka kama sun hada da buhunan shinkafa ‘yar kasar waje 2,681; kwalin taliya 1,421;dilar gwanjo 419, galan din mai 250 hadi da madarar gari 172 da sauran kayayyakin daban-daban daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kwanturolan ya kara da cewa sun tuntubi mazauna garuruwan Maigatari, Jeke da Babura a jihar Jigawa, domin su kara taimakawa jami’an kwastam dake aiki a yankin da bayyanan sirri da zasu taimaka wajen kamo wadanda ke fasa kauri a yankin.

Ya ce tuni rundunar ta yi tanadin matakan tsaro daban-daban da za su tabbatar da cewa kayayyakin da ke shigowa yankunanta na biyan kudaden haraji.

Dauda Ibrahim Chana ya tabbatar da hukumar kwastam ta sanya tsauraran matakan tsaro a duk hanyoyin da aka gano masu fasa kwaurin suna amfani dashi.

Latest stories

Related stories