Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoKudin aikin hajjin 2024 zai iya kaiwa Naira Miliyan 6

Kudin aikin hajjin 2024 zai iya kaiwa Naira Miliyan 6

Date:

Kungiyar masu gudanar da aikin Hajji da Umrah ta kasa, ta koka kan yiyuwar tashin farashin Hajjin badi, inda ta ce maniyyata na iya biyan kusan Naira miliyan 6 sabanin Naira miliyan 3 da aka biya a hajjin bana.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Yahya Suleiman Nasidi ne ya yi wannan tsokaci a Larabar nan, lokacin da yake jawabi a nan Kano yayin taron wayar da kan maniyyata, mai taken “Hajji 2024: Sabbin Kalubale, Dama mara iyaka.”

Nasidi ya nuna damuwarsa kan yadda farashin kudin aikin hajjin zai ninka na shekarar 2023 saboda tashin dalar Amurka.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar alhazai ta kasa, NAHCON da su taimaka wajen sakin kudaden aikin hajjin na shekarar 2024 a kasar Saudiyya.

A cewarsa basu samu wani kaso na dalar Amurka daga gwamnati ba, amma suna ci gaba da gudanar da kasuwancinsu da tare da sauya kudaden ketare.

Don haka ya ce suna tsoron abin da zai faru idan har ba su samu wani dauki daga gwamnati ba.

Alhaji Yahya Suleiman Nasidi, ya yi kira ga masu son zuwa aikin hajjin badi da su yi kokari wajen biyan kudinsu a kan lokaci.

Latest stories

Related stories