Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKAI TSAYE: An dage zaman kotun sauraron karar zaben shugaban kasa

KAI TSAYE: An dage zaman kotun sauraron karar zaben shugaban kasa

Date:

Ya yau ne kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta zauna domin sauraron karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar.

A zaman kotun na yau jam’iyyar PDP da ta bakin lauyan ta Chris Uche SAN, sun bukaci kotun ta bayar da dama a watsar shari’ar kai tsaye a wasu kafafen yada labarai.

Sai dai, Sauran bangarorin da ke cikin shari’ar ba su amince da bukatar  bukatar ba.

Bayan amincewa da muhawara da lauyoyi suka yi a zaman gaban kotun, kotun ta dage zaman zuwa ranar Alhamis 11 ga Mayu, 2023, da karfe 2:00 na rana domin ba wa sauran bangarori, APC, Bola Tinubu da INEC damar mayar da martani ga bukatar PDP da Atiku Abubakar na watsa shari’ar kai tsaye.

HOTUNA: Shugaban riko na jam’iyyar PDP na kasa Amb Iliya Umar Damagum da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Hon Debo Ologunagba da sauran shugabannin jam’iyyar suka isa dakin kotun, yayin da ake jiran karasowar Alkalan kotun.

Latest stories

Related stories