Hukumar kididdiga ta ƙasa NBS ta ce zuwa karshen shekarar 2023 da ta gabata, akwai masu amfani da Internet a Kano guda miliyan 9, yayin da jihohin Lagos da Ogun ke gaban Kano a yawan masu amfani da internet din.
A matakin ƙasa kuwa yawan masu amfani da internet a Najeriya ya Haura miliyan 163 da dubu 800.
Wannan adadi ya haura na shekarar da gabata da kashi 1.35, inda a waccan shekarar ake da mutum miliyan 154 da dubu 800.
Jerin jihohin da sukafi amfani da Internet a Najeriya.
1. Lagos miliyan 18 da dubu 900
2. Ogun miliyan 9 da dubu 500.
3. Kano miliyan 9
4. Oyo miliyan 8 da dubu 4
5. Kaduna miliyan 7 da dubu 400
6. Abuja miliyan 5 da dubu 800
7. Rivers miliyan 5 da dubu 600
8. Adamawa miliyan 5 da dubu 400
9. Katsina miliyan 4 da dubu 600
10. Delta miliyan 4 da dubu 400