Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHar yanzu kotu ba ta bamu umarnin kamo Ado Gwanja ba -...

Har yanzu kotu ba ta bamu umarnin kamo Ado Gwanja ba – yan sanda

Date:

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce har yanzu ba ta samuumarni daga kotu ba na kama mawaki Ado GwanjaAdoA.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyanahakan a shafinsa na Facebook.

A ranar Litinin ne dai, babbar kotun jihar Kano mai lamba biyarkarkashin jagorancin mai shari’a Aisha Mahmud, ta bayar da umarnin a kamo mata mawaki Ado Isa Gwanja.

Haka kuma kotun ta haramta masa yin waka har sai yan sandasun kammala bincike a kansa.
Kotun ta kuma haramtawa Ado Gwanja zuwa gidan biki dominyin waka, sannan kuma ta hana duk wani ko wata ya hauwakarsa a shafukan sada zumunta.

Tin dai a shekarar 2022 ne, majalisar malaman Kano ta yi kararmawakin a kotun shari’ar musulunci dake Bichi ta hannunlauyanta, Barr. Sulaiman Gandu, bayan da Gwanja ya yi watawaka mai suna “WAR.”

Majalisar ta ce wakar akwai kalaman batsa a cikinta kuma za ta iya bata tarbiyyar yara a nan Kano.

A wancan lokacin kotun ta bada izini a kamomawaki ado Gwanja, amma sai ya garzayababbar kotun shari’ar Musulunci mai lambabiyar ya kuma karbo takardar da ta hana a kamashi a wancan lokacin.

A zamanta na ranar Litinin, kotun karkashinjagorancin mai Shari’a Aisha Mahmoud ta badaumarnin a kamo Ado Gwanja, sannan ta ce ta haramta masa yin kowacce irin waka har saiyansanda sun kammala bincike kan zargin da malaman Kano suke yi masa.

Sai dai rundunar yan sandan Kanon, ta ce da zarar ta samuumarnin to za ta kamo mawaki Gwanja.

Latest stories

Related stories