Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Iyalan fasinjojin jirgin kasan da aka sace na zanga-zanga a Abuja.

‘Iyalan fasinjojin jirgin kasan da aka sace na zanga-zanga a Abuja.

Date:

Bayan sakin sabon video da maharan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sukayi wanda ke nuna yadda suke dukan fasinjojin da sukayi garkuwa dasu, ‘yan uwa da iyalan wadanda aka sace sun mamaye ma’aikatar sufuri ta kasa inda suke zanga -zanga domin gwamnati ta kubutar musu da ‘yan uwansu.


A safiyar ranar Litinin ne masu zanga-zangar suka hana ma’aikatan shiga ofisoshin su inda sukace bazasu bar harabar gurin ba har sai an kubutar musu da ‘yan uwansu.

Masu zanga-zangar dai na rike da kwalaye wanda ke nuna cewa sun gaji da jira ‘yan uwan na cigaba da kasancewa a hannun ‘yan ta’addar.

Harin Kaduna: Majalisar wakilai ta gayyaci shugabanin tsaron kasar nan
Wasu kwalayen dai na dauke da rubuce rubuce kamar su “Dan Allah shugaban kasa ka taimakemu”, Gwamnatin jihar Kaduna ki sakar mana ‘yan uwanmu; Bama iya bacci da idanuwan mu guda biyu.

Tsaro: Za a nada dan ta’adda sarauta a Zamfara
Sai dai har kawo yanzu ministan sufuri na kasa Rotimi Amaechi ko ma’aikatar tsaro ta Kasa basuce komai akan sabon vidiyon da ‘yan ta’addar suka fitar ba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...