Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBan taba nadamar zaman dan sanda ba-Kwamishinan Kano mai ritaya

Ban taba nadamar zaman dan sanda ba-Kwamishinan Kano mai ritaya

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kwamishinan Kano mai barin gado Sama’ila Shua’aib Dikko ya ce bai taba nadamar zama dan sanda ba cikin shekaru 35 din da yayi yana aiki.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi bankwana ga yan sandan jihar Kano ranar Litinin.

Kwamishinan wanda lokacin ritayarsa ya yi ya ja hankalin Yan sanda da su kauracewa ayyukan da za su bata sunansu da na rundunar.

Ya kuma yabawa manyan Jam’ian yan sandan Kano bisa hadin kan da suka bashi lokacin da yake aiki.

A cewarsa hadin kan jam’ian yan sandan da suka bashi shi ne ya kai shi ga dukkan nasarar da ya samu.

Ya kuma bukaci dukkanin ‘yan sandan da ke jihar nan su kasance jakadu nagari a duk Inda suka tsinci kansu.

Ya kuma yaba da irin hadin kan da sauran Jam’ian tsoron jihar nan ke da shi, a cewarsa ba dan hadin kansu ba da bai Kai ga gaci ba.

“Ina jan hankalinku da ku zama cikin shiri ko da yaushe, saboda Koda yaushe yan ta’adda na bin diddigin ku.

“Idan kuka yi sake za su cimmuki alhalin ba kwa cikin shiri” A cewarsa.

Kwamishinan ya kuma godewa babban sifeton yan sandan kasar nan bisa damar da ya Bashi.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...