Saurari premier Radio
24.7 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDuk da matsalar tsaro Shugaba Buhari zai tafi Liberia a Talatar nan

Duk da matsalar tsaro Shugaba Buhari zai tafi Liberia a Talatar nan

Date:

Duk da matsalar tsaro shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Liberia, halartar bikin cikarta shekaru 175 da samun ‘yancin kai.

Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, ne ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.

Garba Shehu, ya ce Buhari zai kasance amatsayin bako na musamman inda zai hadu da sauran shugabannin kasashen duniya domin taya al’ummar kasar ta Liberia murna.

Taken bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan shine “samar da hadin kai da tabbatar da zaman lafiya domin cigaba”.

Abinda baku sani ba dangane da kwalejojin Kimiyya da ke Kano – Rahoto
A shekara ta 2019 kasar Liberia ta karrama shugaba Buhari da lambar yabo mafi girma a kasar bisa gudunmawa da kasar nan take baiwa kasar ta Liberia.

Shugaba Muhammadu Buhari dai zai samu rakiyar ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama da daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NIA) Ambasada Ahmad Abubakar.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...