24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin KanoASUU: Gwamnatin Kano zata kawo karshen yajin aikin malaman Jami'a

ASUU: Gwamnatin Kano zata kawo karshen yajin aikin malaman Jami’a

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na kawo karshen matsalar yajin aikin malaman jami’a da kungiyar ASUU ke yi a halin yanzu.

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin wani tattaki da kungiyar kwadago tayi zuwa fadar gwamnatin Kano da a ranar Talata.

 

ASUU-Kungiyar Kwadago za ta tsunduma yajin aiki

Abdullahi Umar Ganduje, na cewa magance matsalar yajin aikin ya zama wajibi duba da nakasun da aka samu a bangaren ilimi.


Ganduje ya ce za su taimaka da shawarwarin da suka kamata wajen ganin matsalar ta zama tarihi.

 

Ya kuma kara da cewa, shakka babu Gwamnatin Kano tayi rawar gani wajen ci gaba da biyan malaman jami’oi dake aiki a jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil da ta Yusuf Maitama Sule, wanda tuni tsari yayi nisa wajen magance matsalolin da suka bijiro da su.

 

Da yake jawabi tun da fari, shugaban kungiyar kwadago na jihar Kano, Comrade Kabiru Ado Minjibir na cewa, tattaki na kafa da kafa na zuwa ne don mika koken su ga Gwamnatin Kano kan halin da ‘yan kungiyar ASUU ke ciki, da ya kamata a baiwa muhimmanci sosai.

 

Minjibir ya kuma bukaci ‘yan kungiyar da su zauna lafiya tare da bin doka da oda don baiwa Gwamnatin damar aiwatar da nata bangaren.

Latest stories