Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Monday, December 11, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKAROTA: ta kama wasu matasa da makamai da kayan shaye-shaye a Kano

KAROTA: ta kama wasu matasa da makamai da kayan shaye-shaye a Kano

Date:

Hukumar KAROTA ta kama wasu bata garin matasa da makamai da kuma kayan shaye-shaye a shatale-talen gadar Dangi da ke birnin Kano.

 

Mai Magana da yawun hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Naisa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Talata .

 

Nabilusi Abubakar, ya kuma ce guda cikin wadanda hukumar ta kama mai suna Mas’ud Ya’u Yusuf, ya shaidawa hukumar KAROTA cewa an kama su da su ne da kayan shaye-shaye da makamai.

 

Jami’an sintiri na hukumar ta KAROTA ne suka sami nasarar cafke matasan da daddare a karkashin shatale-talen Dangi, inda mutanen da aka kama suka bayyana akalla sun kai kwanaki hudu da shigowa garin Kano.

Ba jami’in mu ne ke shan giya a wani faifan bidiyo ba- KAROTA

Sai dai binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa matasan sun shigo jihar Kano ne daga jihohin Katsina da Zamfara.

 

Tuni dai KAROTA ta bayyana bayan kammala binke ta mika mtasan hannun jami’an Yan sanda na ‘Yar Akwa domin faɗaɗa bincike tare da daukar mataki na gaba.

Latest stories

Jihar Kano ta samu lambar Zinare ta farko a gasar Para Games ta 2023

Ahmad Hamisu GwaleDan wasa Adeleke Abajoye Odunaya, ya jagoranci...

Related stories

Jihar Kano ta samu lambar Zinare ta farko a gasar Para Games ta 2023

Ahmad Hamisu GwaleDan wasa Adeleke Abajoye Odunaya, ya jagoranci...