Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin gado: Iyalan Nababa Badamasi sun gurfanar da yayunsu a EFCC

Rikicin gado: Iyalan Nababa Badamasi sun gurfanar da yayunsu a EFCC

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Iyalan fitattaccen attajiran nanda ke Kano, Alhaji Nababa Badamasi na ci gaba da nuwa juna yatsa bayan da suka yi zargin manyan yan uwansu da yi musu rufda ciki a gadonsu.

Wannan na zuwa ne bayan da kananan ‘yayan suka zargi manyansu uku da suka hadar da Alhaji Tijjani Nababa da Alhaji Sunusi Nababa da kuma Alhaji Zubairu Nababa.

Iyalan nasa sun shigar da kara ne hukumar ta EFCC bisa zargin manyan sun sayar musu da wani kamfani da mahaifinsu yam utu ya bari mai suna Gaskiya Textile.

A cewarsu an sayar da kamfanin da ke da magada da yawa kan kudi da ya haura Biliyan biyu.

Guda daga cikin magadan da ta nemi a sakaye sunanta ta ce, haka kawai babu shawarsu manyan yayyen nasu suka sayar da da kamfanin mallakin maifinsu.

A cewarta sun sayarwa da wani da ake kira Abduqadir Alasan Dantata, wanda kafin nan sai da suka tura masa da takardar kar ya siya saboda na gado ne amma ya kekasa kasa yaki.

“Shi wanda ya siya da ake kira Abdulqadir Sunusi Dantata, sai da muka tura masa takarda a rubuce ta hannun lauyan mu kan kada ya  siya amma ya kauda kai.

“Muna sanar da shi inda mai wannan kaya ya tafi shima zai tafi don haka ya kamata ya kalli halin da suke ci amma yaki.

Shi ma daya daga cikin Magadan da ya zanta da Premier Radio jim kadan bayan shigar da korafinsu a hukumar EFCC ya ce ba wannan ne karon farko da manyan yayyun nasu ke yi musu irin wannan kama karyaba.

Ya ce sun ja hankalinsu akan kamfanin da hakkin da yake ciki amma aka nuna musu su yara ne basu da abin cewa.

Munyi kokarin jin ta bakin manyan nasu bayan da muka kirasu ta wayar taroho inda suka ce idan sun tattauna da lauyoyinsu za su yi mana Karin haske a nan gaba.

Latest stories

Related stories