Saurari premier Radio
41.8 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin gado: Iyalan Walin Daura na rigima a gaban kotu

Rikicin gado: Iyalan Walin Daura na rigima a gaban kotu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Iyalan Walin Daura Alhaji Sani Buhari Daura sun gurfanar da manyan yan uwansu a gaban kotu bisa zargin kartakar da wasu kadarorinsu ya yin da suke neman a raba musu gado.

Sun dai shigar da karar ne a gaban kotun musulunci da ke filin hoki inda suke neman kotun ta kwato musu hakkokinsu a hannun manyan nasu.

A cewar masu kara manyan gidan na kokarin yi hafzi da wasu manyan wurare da suke ikirarin ba na mahafinsu ba ne kuma ba za a sa su a gado ba.

Ya yin da su kuma kan kanan ke cewa manyan na kokarin kwace musu dukiya ne kawai ta karfin tsiya.

Sai dai a zaman kotun na ranar Talata, Alkalin Kotun Abdullahi Halliru ya saurari bayan bagarorin biyu, ya kuma ja hankalin lauyoyi kan su daina cakuda al’amura.

Sai dai lauyan da ke kare ‘yan kan-kanan Muhammad Adhama ya ce suna neman kotu ta kwato musu hakkokinsu ta hanyar rana gado.

Ya ce sun shigar da korafinsu gaban kotun sun kuma gudanar da roko a gabanta kan bukatunsu na a fito da dukiyar mahaifan wadanda suke karewa a raba kamar yadda addinin musulunci ya tana.

Sai dai kuyoyin manyan sun sake shigar da kara gaban babban kitun jiha kan ta dakatar da kotun musuluncin daga ci gaba da sauraron shari’ar.

A cewarsu akwai bukatar da suke da ita a gaban kotun tarayyar a don haka a dakatar da neman hakkin kananan har sai waccan kotu ta biya musu bukatunsu.

Jim kadan bayan fitowa daga kotun ne kuma premier Radio ta yi kokarin jin ta bakin lauyan manyan gidan sai sai sun ce sub a za su yi Magana da yan jarida ba.

Tuni dai Alkalin kotun ya sanya ranar 9 ga Agustan 2022 wato makwanni biyu masu zuwa domin ci gaba da sauraron karar.

Latest stories

Related stories