Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwanaki 70 kenan bamu da wutar lantarki- Hausawan jihar Oyo

Kwanaki 70 kenan bamu da wutar lantarki- Hausawan jihar Oyo

Date:

Hafsat Iliyasu Dembo

Al’ummar Hausawa mazauna unguwar sabo dake jihar Oyo sun koka kan rashin wutar lantarki, inda suka ce kimanin kwana 70 kenan da aka zare musu layin wutar lantarki, ba tare da wani dalili ba.

Shugabar mata mazauna kudancin kasar nan Hajiya Aisha Ismail ce tayi koken a zantawar ta da manema labarai.

Hajiya Aisha tace unguwar su ta sabo suna samun wutar lantarki a koda yaushe saboda ta nan wayar wutar garin ta biyo, amma haka kawai rana daya aka cire fuse din wutar ba tare da wani dalili ba.

Tayi kira ga mahukunta da su kawo masu dauki duba da cewa da wutar lantarkin suka dogara wajen gudanar da kasuwancin su wanda suke samu su rike kan su da iyalan su.

Tace unguwar ta sabo galibin mazauna yankin Hausawa ne wadanda suka fito daga jihohi daban daban dake arewacin kasar nan.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...