Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Saturday, February 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniHAJJIN BANA: Jihar Kano za ta fara dawo da Alhazan ta

HAJJIN BANA: Jihar Kano za ta fara dawo da Alhazan ta

Date:

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce a Talatar nan take sa ran karbar jadawalin yadda za a fara aikin jigilar dawo da alhazan ta gida Najeriya.

Babban Sakataren Hukumar Muhammad Abba Dambatta ne ya sanar da hakan a garin Makkah yayin ganawarsa da manema labarai.

Ya ce bayan da suka rubutawa Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON takarda, ta ce a ranar 26 za ta bayar da yadda jadawalin tashin jiragen zai kasance.

Danbatta ya kara da cewa yanzu haka sun gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki dan ganin yadda za a fara aikin jigilar Alhazan da suka je Makkah a jirgin karshe don kai su birnin Madina domin su yi ziyara.

Latest stories

Related stories