Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRashin tsaro ya janyo karancin masu karbar katin zabe a Katsina-INEC

Rashin tsaro ya janyo karancin masu karbar katin zabe a Katsina-INEC

Date:

Hukumar zabe ta kasa INEC, ta ce matsalar tsaro ne dalilin da ya janyo karancin masu fitowa karbar katin zabe a jihar Katsina.

Kwamishinan hukumar a jihar Katsina Jibrin Zarewa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a jihar.

Yace ba ko wanne yanki hukumar ke iya tura jami’an ta, don yiwa mutane rijistar katin zaben ba.

A cewa sa suna fargabar matsalar zata iya shafar jami’an nasu.

Ya ce a yanzu haka cibiyoyin da suke bada katin ma akwai karancin fitowar mutane saboda tsoro.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin da hukumar zaben ta kasa ta bayyana, a matsayin wadda aka samu karancin masu fitowa karbar katin zabe, duk da kasancewar ta ta hudu a yawan al’umma a kasar nan.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories