24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGuguwa mai karfi ta rusa gidaje sama da 100 a Danbatta

Guguwa mai karfi ta rusa gidaje sama da 100 a Danbatta

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Wata guguwa mai karfi ta yi sanadiyyar rasuwar wata mata tare da jikkata wasu da dama a karamar hukumar Danbatta.

 

Shugaban karamar hukumar Alhaji Mohammad Abdullahi Kore ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi tawagar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano.

 

Kore ya ce al’amarin ya faru ne a yankunan Unguwar Bai da Dukawa, wanda ya janyo sanadiyyar rushewar gidaje 70 a yankin.

 

Ya kara da cewa karamar hukumar ta dauki nauyin jinyar wadanda suka jikkata tare da alkawarin daukar matakan kare afkuwar hakan a nan gaba.

HOTUNA

 

A nasa bangaren, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Kano Sale Aliyu Jili ya jajantawa wadanda ibtila’I ya rutsa da su, baya ga basu tallafi.

 

Shima da yake jawabi, wakilin dagacin Dukawa Sani Ibrahim, ya ce sun samu tallafi daga wasu masu hannu da shuni bayan faruwar al’amarin.

 

Mahukunta dai na ci gaba da yin kira ga al’umma da su cigaba da tsaftace magudanan ruwa domin kare kai daga faruwar ambaliyar ruwa.

Latest stories