Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoAbinda baku sani ba dangane da kwalejojin Kimiyya da ke Kano –...

Abinda baku sani ba dangane da kwalejojin Kimiyya da ke Kano – Rahoto

Date:

Umar Idris Shuaibu 

Tun bayan kafa Kwalejojin kimiyya a tsohuwar jihar Kano da ake yi wa lakabi a turance da ‘Dawaki Experiment’, a zamanin mulkin Gwamnan Soja Kanal Sani Bello mai ritaya, makarantun suka ci gaba da yaye kwararru a bangarorin kimiyya daban-daban, dama sauran bangarori a jihar Kano har ma da kasa baki daya.

Sai dai an samu sauye-sauye da dama daga wancan lokacin zuwa yanzu.

Manufar kafa kwalejojin kimiyyar da ke tsohuwar jihar Kano a shekara ta 1977 ya zuwa yanzu bai wuce shirya daliban da ake son su zama kwararrun likitoci da Injiniyoyi da sauran kwararru a fannoni daban-daban a manyan makarantu da jami’oi ba.

Wannan mafarki ya zama zahiri kasancewar galibin daliban kwalejojin kimiyyar ne suka mamaye manyan ma’aikatun gwamnati da asibitoci da sauran wurare masu zaman kansu a jihar Kano, har ma da kasashen ketare.

Sai dai a yanzu kwalejojin da dama na fuskantar koma baya sakamakon rashin kulawar masu ruwa da tsaki da gwamnati a tsawon lokacin da suka yi.

Wani dalibi da ya yi karatu a daya daga cikin kwalejin, Ibrahim Kabir ya bayyanawa Premier Radio cewa an samu koma baya ainun a sha’anin tafikas da wadannan kwalejoji.

A cewarsa wannan ya faru ne sakamakon wasarere da gwamnati ta yi da su a wadannan shekarun.

Shi kuwa shugaban kungiyar tsofaffin daliban kwalejojin ta KASSOSA, Malam Balarabe Nuhu Jalla Dambatta ya ce shugabancin su ya maida hankali ne wajen dawo da martabar wadannan makarantu dake jihar Kano, da sauran sassa da suke da alaka ta kai tsaye da su.

“Zuwan mu kan wannan shugabanci mun yi kokarin tafiya akan wasu manufofi shida da muka yi ittifakin za su taimaka mana wajen shawo kan matsalolin.

“Tun da fari dai rashin baiwa hukumar kula da makarantun muhimmanci daga bangaren gwamnati ya taimaka, da kuma tsari da suke da shi na cin gashin kansu a bangarori daban.

“Wadannan manufofi sun taimaka wajen kafa kwamitoci da za su yi aiki ba dare ba rana wajen nemo kudi daga mambobinmu da za mu yi aikace-aikacen gyara makarantun.

“Sai kuma kwamitin da zai tattara alkaluman yawan mu, da kwamitin bada tallafin karatu ga dalibai hazikai da ba su da damar ci gaba da karatu.

“Akwai kuma kwamitin da zai maida hankali wajen gina sakatariyar kungiyar KASSOSA ta din-din-din, da dai sauran su’’, a cewar Balarabe Nuhu Jalla Dambatta.

A nasa bangaren, shugaban hukumar da ke kula da makarantun, Alhaji Ahmad Tijjani Abdullahi ya ce matsalolin sun samo asali ne sakamakon dimbin aikace-aikace da yayiwa gwamnati yawa.

“Idan ka duba kwalejojin sun karu ba kamar a wancan lokacin ba, haka zalika yawan daliban ma ya karu matuka, wadannan na daga cikin dalilai masu karfi da ya kawo koma bayansu.

“Sai dai a matsayin mu na hukuma zamu ci gaba da yin aikace-aikace ganin makarantun nan sun rike kambun su da aka san su da shi a baya, ta yadda jihar Kano dama kasa baki daya za a ci gaba da alfahari da daliban mu.

Alhaji Ahmad Tijjani Abdullahi ya kuma kara da cewa, duk da yake akwai matsaloli da ake samu na yau da kullum, amman za su ci gaba da bada kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa tare da bin diddigin matsaloli da suke kawo nakasu.

“A watannin baya an samu matsaloli na bangaren koyarwa wanda hukumar mu bata dauki abin da wasa ba, wajen hukunta malaman da aka samu da aikata wadannan laifuka”.

A yanzu dai banda ainihin kwalejin kimiyya ta Dawakin Kudu da Dawakin Tofa, an samu karin wasu kwalejojin a fadin jihar Kano.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories