Premier Radio 102.7 FM
Gwamnatin Kano Kano Labarai

Yarbawa sun sa ke nada Ganduje sarauta

Mukhtar Yahya Usman

Majalisar Malamai ta jihohin Yarbawa ta baiwa gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje sarautar Alaudden of Yoruba

Wanan na zuwa ne kwanakin biyu bayan da Alafin na Oyo ya nadashi da matarsa sarautar Aare Fiwajoye and Yeye Aare Fiwajoye na kasar Yarubawa.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimakin na musamman ga gwamnan kan al’amuran daukar hoto Aminu Dahiru ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta nuna gwamnan ya sake samun sabuwar sarautar ne a ranar Asabar 18 ga Yuni da muke ciki.

Shugaban majalisar limamai da malamai na Jihar, Oyo Sheikh Abdulganiyyu Abubakar ne ya nada gwamnan a madadin limanan.

Da yake jawabi Sheikh Abdulganiyyu ya ce ana bayar da sarautar ne ga Musulmi mai riko da addini da kuma yi wa addinin hidima.

A cewarsu binciken su ya tabbatar musu Gwamna Ganduje ya cika wandannan sharuddan.

A Wani Labarin...

Max Air ne zai yi jigilar mahajjatan Kano a bana

Mukhtar Yahya Usman

Rikicin APC: Banza bakwai ta shuka dusa -Ganduje

Mukhtar Yahya Usman

Dokar kananan yara:Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani

Mukhtar Yahya Usman