Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCIVIL DEFENCE: Ku sanar da duk wani motsi da baku yarda dashi...

CIVIL DEFENCE: Ku sanar da duk wani motsi da baku yarda dashi ba

Date:

Rundunar tsaro ta Civil Defence reshen jihar Kano ta bukaci al’umma dasu sanarwa da hukumomi duk wani motsi da basu yarda dashi ba.

Shugaban hukumar a nan Kano Adamu Idris Zakari, ne ya bayyana haka yayin ziyarar da yakai majalisar dokokin jihar Kano a Talatar nan.

Ya ce matsalar tsaro ba iya ta jami’an tsaro ce kawai akwai bukatar mutane su bada tasu gudunmawar domin dorewar zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.

Ya ce kan hukumomin tsaro a jihar Kano a hade yake kuma wannan ce ta sanya Kano ke cigaba da kasancewa daga cikin jihohin dake masu zaman lafiya.

Matsalar tsaro:Malisar wakilai ta yi barazanar tafiya yajin aiki

Shugaban hukumar ta Civil Defence, Adamu Idris Zakari, ya bukaci al’ummar jihar nan dasu cigaba da baiwa hukumomin tsaro hadin kai a koda yaushe domin cigaba da samun dauwamamen zaman lafiya.

Latest stories

Related stories