Saurari premier Radio
25.1 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoZa mu tsaftace kasuwannin Kano daga gurbatattun kaya - Dan Agundi

Za mu tsaftace kasuwannin Kano daga gurbatattun kaya – Dan Agundi

Date:

Umar Idris Shuaibu

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta wajen dawo da martabar hukumar kula da hakkin mai saye ta jihar.

Mai rikon mukamin shugabancin hukumar Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da jami’an hukumar bayan kama aikisa.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sake shi a matsayin mai rikon mukamin shugaban hukumar.

Dan Agundi ya ce ya sha alwashin yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin ya dawo da karsashin aikin hukumar saboda muhimmancin da yake da shi a tsakanin al’umma.

Shugaban ya kuma kirayi  al’ummar jihar Kano da su ci gaba da basu goyon bayan da ya kamata don yin nasara akan aikin da aka sa gaba.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...