33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiDaliban Kano dubu 15 na cikin barazanar rasa jarrabawar NECO

Daliban Kano dubu 15 na cikin barazanar rasa jarrabawar NECO

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Ahmad Hamisu Gwale

Akalla daliban Kano dubu goma 15 ka iya rasa rubuta jarrabawar NECO da ake shirin fara gudanarwa a ranar Litinin dinnan 27 ga Yunin da muke ciki.

Tuni hukumar shirya jarrabawar NECO ta kammala shirin fara gudanar da jarrabawar a dukanin jihohin kasar nan daga ranar Litiinin mai zuwa.

Daliban Kano kimanin dubu 15 ne ka iya fuskantar gaza rubuta jarrabawar, biyo bayan kudin da NECO ta bayyana tana bin gwamnatin Kano har kimanin Biliyan daya da dubu dari biyar.

A zantawar wakilin Premier Radio Ahmad Hamisu Gwale da masanin ilimin zamantakewar dan Adam Dakta Idris Salisu Rogo Malami ne a jami’ar Bayero dake Kano yace lamarin abin takaici ne kuma zai iya kawowa ilimin jihar nakasu.

‘Matuka akwai takaici yadda aka samu jinkirin biyan kudin da NECO kebin gwamnatin Kano, wanda kuma lamarin zai sanya jihar ta kara samun koma baya a ci gaban ilimin jihar’, a cewar Idris Salisu Rogo.

Koda muka tuntubi Sakatariya a hukumar Ilimi ta jihar Kano wadda Hajiya Lauratu Ado Diso ke jagoranta bamu samu ji daga gare taba, sakamakon kin shiga da wayar ta takiyi.

Kuma a gefe guda mun aika mata da sakon karta kwana, amma har kawo yanzu bata bada amsar sakon da muka aike mat aba.

Latest stories