Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNeman Maza: Kotu ta yi umarnin jefe wasu mutum uku

Neman Maza: Kotu ta yi umarnin jefe wasu mutum uku

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Wata kotun shari’ar musulunci a jihar Bauchi ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

Alkalin kotun da ke zamanta a Ningi Mika’il Sabo ya kama mutane ukun da laifin aikata neman maza.

Mutane ukun sun hadar da Abdullahi Abubakar Beti da Kamilu Ya’u sai Mal. Haruna dattijo mai shekaru 70.

Alkalin ya ce laifin da suka aikata ya saba da sashe na 134 na dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Bauchi.

Ya kara da cewa Hakan ya ci karo da Fiquhussunah juzu’i na 2 shafi na 362.

A don haka ne alkalin kotun ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...