Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCin zarafi:Civil Defence a Kano ta kama wasu ma'aurata biyu

Cin zarafi:Civil Defence a Kano ta kama wasu ma’aurata biyu

Date:

Umar Idris Shuaibu

Rundunar tsaro ta Civil Defence ta kama wasu ma’aurata biyu bisa zargin  dukan kawo wuka  da suka yiwa ‘yar aikin su.

Yarinyar mai suna Nana Sha’una Yusuf mai  shekaru 14, ta dade tana shan azaban a hannun iyayen gidan nata.

A cewar rundunar iyayen gidan nata su ne Ahmad Abdulkarim da Safiyya Shamsuddeen da ke zaune a Unguwar Na’ibawa ‘yan Katako.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Idris Abdullahi ya aikewa Premier Radio.

Binciken da rundunar Civil Defence ta gudanar na nuni da cewa magidantan sun rika azabatar da Nana har sai da bayanta ya cika da alamun tabo na duka.

A yazu haka yarinyar wadda yar asalin Kazauren Jijar Jigawa ce na ci gaba da samun kulawar jami’an lafiya tun bayan da rundunar tsaron Civil Defence ta kama ma’auratan.

Rundunar ta kara da cewa, tuni wadanda ake zargin da tursasa ‘yar aikin su kan abubuwan da basu kamace ta ba, da cin zali aka gurfanar da su gaban kotu bayan amsa laifin su da suka yi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories