Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBashi: Kotu a Kano za ta hukunta Kamfanonin MTN da Glo

Bashi: Kotu a Kano za ta hukunta Kamfanonin MTN da Glo

Date:

Umar Idris Shua’aib

Wata kotun majistire karkashin Alkali Malam Ibrahim Gwadabe ta bukaci wasu kamfanoni da su biya Gwamnatin jihar Kano basukan da take bin su.

Wanann na kunshe cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a a ma’aikatar kasuwanci ta jiha, Sa’adatu Sulaiman ta fitar.

Sanarwar na cewa tuni kotun majistiren ta baiwa kamfanonin wa’adin mako biyu da su gaggauta biyan kudaden ko su fuskanci hukuncin kotu.n

Kamfanonin da za a hukunta kan gaza biyan gwamnati basukanta sun hadar da  MTN  Glo, da bankunan Titan da Aso Savings, da Veritas Pension, da kuma kamfanin fiton kayayyaki na Maersk.

Wannan na zuwa ne bayan da ma’aikatar kasuwanci, masana’antu, kungiyoyin gama kai da ma’adanai ta jiha ta yi karar kamfanonin, bisa gaza biyan kudaden sabunta harkokin kasuwanci na jiha.

Laifin dai ya saba da sashe na 8 da 9 na dokar gudanar da kasuwanci da rajistar sa na jihar Kano na shekara ta 2014.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...