Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSakatare janar na OPEC Barkindo ya rasu

Sakatare janar na OPEC Barkindo ya rasu

Date:

Ibrahim Hassan Hausawa
Babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC), Mohammed Sanusi Barkindo, ya rasu.

Manajan Daraktan Kamfanin Mai na kasa NNPC Mele Kyari, ne ya sanar da rasuwar tasa a shafinsa na twitter ranar Laraba

Kyari ya ce ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren ranar Talata nan

Hakan na zuwa ‘yan sa’o’i kadan bayan ya gabatar da jawabi ga masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas a taron da aka gudanar kan sanin mai da iskar gas na Nijeriya na shekarar 2022 a Abuja.

Bayan kammala taron ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati tare da tawagar sakatariyar kungiyar OPEC.

Ya rasu yana da shekaru 63.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories