33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAn jikkata mutum biyu a harin da aka kaiwa motocin Buhari

An jikkata mutum biyu a harin da aka kaiwa motocin Buhari

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...
Mutane biyu aka jikkata  bayan da yan ta’adda suka farmaki jerin gwanon motocin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a cewar fadar shugaban kasa.

A daren jiya ne dai wasu yan ta’adda suka farmaki motocin a garin Dutsenma a hanyarsu ta zuwa Daura daga Abuja don tarar shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Fadar shugaban kasar ta tsara cewar shugaba Buhari zai yi sallar idi ne a garin Daura mahaifarsa.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ya ce mutane biyu ne sukaji rauni yayin harin.

Ya ce tuni aka garzaya da su Asibiti a ke kuma basu kulawa ta musamman.

Haka kuma fadar shugaban kasar ta nuna rashin Jin dadinta kan wannan hari.

Latest stories