Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHawan Nasarawa:Dalilin da ya sa Ganduje bai karbi sarkin Kano ba

Hawan Nasarawa:Dalilin da ya sa Ganduje bai karbi sarkin Kano ba

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta ce wani muhimmin taro da gwamnonin kasar nan da Ganduje ya halarta a Abuje ne dalilin da ya sanya bai karbi sarkin Kano a Hawan Nassrawa ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce taron da gwamnan ya tafi babu makawa sai yaje da kansa, kana daga bisani ya wuce yayiwa shugaba Muhammadu Buhari bayani kan taron.

Muhammad Garba ya ce wadanda ya kamata su karbi gwamnan a madadinsa su ne mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da kuma kakakin Majalisar Kano Ibrahim Chidari wanda yanzu haka duk suna kasa mai tsarki.

Haka kuma mutum na uku da ya Kamata ya karbi sarki shi ne sakataren gwamnati Alhaji Usman Alhaji wanda shi kuma hakimi ne a masarautar Gaya, da ake ganin ba a girmama sarkinba idan aka ce ya karbeshi.

Sanarwar ta kara da cewa sai da gwamnan ya tattauna da Sarkin kan halin da aka tsinci kai ya kuma baiwa sarkin damar ya yi Hawan ya kewaya Inda aka saba bi don gaisawa da jama’a.

A don haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita jitar da ake yadawa cewa gwamnan da gangan ya ki karbar sarkin

Inda ya ce kafin wanann al’amri ya faru gwamnan ya gaisa da Sarkin a Masallacin Ida da gidan Shattima ya kuma je Hawan Daushe da hakan ke nuna babu matsala.

 

 

Latest stories

Related stories