Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNayi aikin hajji a Kano ne don na debewa maniyyata kewa-Miniyyaci

Nayi aikin hajji a Kano ne don na debewa maniyyata kewa-Miniyyaci

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wanni maniyya ci daga karamar hukumar Gezawa Malam Jibril Abdu ya ce ya gudanar da aikin hajji a sansanin alhazan Kano ne dan ya debewa maniyyatan da aka tafi aka bari kewa.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai jirgi ya tafi ya bar Malam Jibril da sauran maniyyata a sansanin alhazan Kano.

Kwatsam sai aka ganshi ya sanya harami ya kuma fara aikin hajjinsa a sansanin Alhazain.

Wanann al’amari dai ya dauki hankulan jama’a sosai Inda maniyyatan da ke cikin bacim rai suka koma dariya.

Ya Sanya harami ne kuma ya ce shi tuni ya fara gudanar da aikin Hajjin nasa.

Abdu, ya ce yanayin da ya shiga na damuwa ne ya sa shi yin alwala ya yi Sallah sannan ya fara gabatar da aikinsa da tunanin hakan zai saukaka masa damuwa.

“Yadda hankulan jama’a suka tashi, kowa na cikin damuwa, ana ta kuka ana ta tsinuwa ya sa na yi wannan shigar don jan hankulan mutane ko sa samu sauki.

“Alhamdulillah, hakan ya yi tasiri kwarai da gaske domin na ga mutanen da ke kuka sun koma dariya.”

Sai dai ya bayyana cewa bai samu damar zuwa ya karasa aikin Hajjin nasa ba saboda ba ingantacce ba ne kuma Kano ba Saudiyya ba ce.

“Allah Bai kira mu ba. Wadanda suka samu damar zuwa kuma Allah Ya dawo da su cikin koshin lafiya, Ya kai mu wata shekarar cikin koshin lafiya.”

 

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...